Me ka ke nema?


Shafin Farko

Yadda Ake Bulog


Mai karatu, ka taki sa'a. A wannan darasi za ka koyi yadda za ka sayi adireshin Intanet haɗe da sararin da za ka adana shafukanka na Intanet. Ga matakan da za ka bi kamar haka:

  1. Latsa wannan hoton da yake ƙasa.
    Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG

    Hoto na ƙasa zai bayyana:

  2. Tura shafin zuwa ƙasa har sai ka ga hoto na ƙasa:

    Lura da waɗannan abubuwan guda uku:
    (1) Soldier
    (2) Minister
    (3) King
    Dukkaninsu sunaye na tsarurrukan gurabe ko filayen hayar adana shafukan Intanet. Tare da zamowar 1 mafi ƙarancin kuɗi, 2 a sama da shi, 3 kuma mafi girma. Iya kuɗinka iya shagalinka. Sai dai, akwai wasu abubuwa da ya kamata ka lura da su wajen saye ko karɓar wannan fili na haya. Latsa nan domin jin yadda aka haihu a ragaya:
    Sannan kuma dai, sai ka sake lura da waɗannan gurabe:
    (a) Gurbin zaɓin adadin watanni ko shekarun da za a biya na haya.
    (b) Madannin amincewa da zaɓi.
  3. Latsa Gurbin (a) ka zaɓi: 1 Year at N3600 (20% OFF)
  4. Latsa Madannin Order (b) Ka saya. Shafi na ƙasa zai bayyana:

    A nan, za ka lura da abubuwa uku:
    (1) Shi ne gurbin da za ka rubuta sunan adireshinka na Intanet; wato adireshin shafin da ka ke so mutane su riƙa ziyartarka da shi. Misali: maidarasu
    (2) Gurbin da za ka zaɓi ɗangon adireshin naka. Kamar irin su .com, .com.ng, .org da sauransu. A wannan darasin za ka ɗauki .com.ng, idan har ka aikata haka daidai, za ka ga daga ƙarshe ka samu wani abu makamancin wannan: maidarasu.com.ng
    (3) Latsa wannan madannin ka ci gaba, za ka ga hoto na ƙasa ya bayyana:

    A wannan gaɓar, za ka lura da waɗannan abubuwan:
    (1) Shi ne sunan adireshin shafinka.
    (2) Shi ne ɗangon sunan adireshin shafin.
    (3) Shi ne cikakken adireshin shafin (Misali, maidarasu.com.ng). Alamar da ke dama da shi kuma tana gaya maka cewa, ka yi nasarar samun wannan suna ba a rigaye ka ba.
    (4) Latsa wannan madannin ka ci gaba. Shafi na ƙasa zai bayyana:
  5. Latsa madannin Add to Cart ka ci gaba. Shafi na ƙasa zai bayyana:

    Shi wannan shafin, yana baka tabbaci ne cewa, ka samu nasarar yin rijistar wannan adireshi na tsawon shekarun da ka karɓa.
  6. Latsa madannin Continue to Final Checkout Page >>>>. Shafi na ƙasa zai bayyana:

    Lura da waɗannan guraben:
    First Name: Rubuta sunanka a gurbin da yake dama da shi
    Last Name: Gurbin rubuta sunan mahaifi.
    Company Name: Sunan kamfaninka, idan akwai, idan kuma babu kana iya rubuta koma wane irin suna ne.
    Email Adress: Rubuta adireshin Imel ɗin da za ka karɓi saƙo a gurbin
    Password: Rubuta mabuɗin da za ka riƙa shiga shafin kwastoma da za su buɗe maka a nan gaba
    Confirm Password: Sake rubuta mabuɗin kamar yadda yake a sama
    Ina baka shawara da cewa, ka samu wata takarda ka rubuta wannan mabuɗi naka ka adana. Kar ka yi wasa da shi!
    Address 1: Rubuta cikakken adireshinka.
    Address 2: Kana iya tsallake shi idan babu
    City: Rubuta ƙaramar hukumar da ka ke
    State/Region: Sunan jaha
    Zip: Rubuta _234.
    Country: Rubuta sunan ƙasarka.
    Phone Number: Rubuta lambar wayarka ba tare da sifilin farko ba. Misali 08039648244 sai ka rubuta 8039648244.
  7. Latsa Madannin Continue Shoping ka ci gaba. Shafi na ƙasa zai bayyana:

  8. Latsa madannin Complete Order ka ci gaba. Shafi na ƙasa zai bayyana:

    Madalla, to yanzu kuma sai ka ɗauko katinka na banki; wato ATM card. Ka shigar da waɗannan bayanan:
    (1) Rubuta wasu lambobi guda 16 da ke jikin katin naka daga gaba.
    (2) Rubuta sunan da yake jikin katin. Yawanci yana ƙasan katin.
    (3) Rubuta shekarar da katin zai gama aiki. Misali, za ka ga 02/20. To haka za ka rubuta kamar yadda yake.

    (4) Juya bayan katin, akwai wasu labobi guda uku sai ka rubuta su.

    (5) Rubuta adireshin Imel da za a tura maka bayanan da za ka riƙa amfani da su wajen shiga shafin naka.
    (6) Rubuta Lambar wayar da za a tura maka sako ta cikinta kamar haka +2348039648244.
    (7) Latsa madannin Pay N3690. Shafi na ƙasa zai bayyana:

  9. Latsa madannin Proceed. Shafi na ƙasa zai fito"

    Sai kuma ka ɗan jinkirta kaɗan, zai fito maka da wani shafi mai gurbin rubuta lambobi da kuma madanni makamancin wannan naƙasa:

    Yawwa. To yanzu kuma za su tura maka wasu lambobi zuwa lambar wayar da ka bayar a sama. Idan ka karɓi wannan saƙon, sai ka koma wancan shafi na sama ka rubuta su a gurbin rubutu sannan ka dannan madannin Verify OTP.
    Ina taya ka murna tare kuma da yi maka fatan alheri. Yanzu kai ma ka mallaki adireshin Intanet na ƙashin kanka tare kuma da karɓar hayar gurbin adana bayanai.
  10. Garzaya zuwa Imel ɗinka. Za a tura maka wasu saƙonnin masu yawa. Daga cikin su za ka ga wanda aka rubuta: New Hosting Account Information, to sai ka latsa shi ka buɗe. Lura da waɗannan abubuwa guda uku a cikin saƙon:
    (1) CPanel Login URL: Latsa wannan ka fara aiki: https://host.dkshared3.com:2083/
    (2) CPanel Username: ........
    (3) CPanel Password: ..........
    Waɗannan bayanai su za su taimaka maka wajen shiga shafin da za ka ɗura shafukanka na Intanet waɗanda mutane za su riƙa buɗewa a duniya suna karantawa.
    Gargaɗi:Kar ka kuskura a san na 2 da na 3. Duk wanda ya san wannan, to zai iya buɗe shafinka ya ɗura abin da ransa yake so.

To, yanzu ka kammala sayen adireshi tare kuma da gurbin adana shafukanka. Abu na gaba shi ne shiga shafin naka domin dasa softuwayar WordPress wadda za ta baka damar gina shafukanka na Intanet. Latsa nan ka dulmiya wannan shafin.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub